Jami’an Tsaron Jami’ar Maiduguri  Sun Kai Samame Dakunan ɗalibai Mata

 

Wani hoton bidiyo ya nuna yadda jami’an tsaro suka kai samame dakunan ɗalibai mata na jami’ar Maiduguri inda suka kwashe mutum 38.

Jaridar PRNigeria ta rawaito cewa waɗanda aka cafke sun hada da matan da suka shiga zanga-zanga kan karin kudin makaranta, da rayuwar wahala da suke yi a jami’ar.

Daruruwan dalibai mata ne suka yi zanga-zangar lumana domin nuna adawa da karin kudin makaranta, sai dai jami’an tsaro sun yi ta datse su.

Majiyoyi sun ce anyi ta amfani da karfi domin dakile daliban daga zanga-zangar.

An jikkata dalibai mata da dama a lokacin boren, yayinda aka rawaito cewa jami’an tsaro sun yi ta gallazawa wasu da dorina.

Akalla an cafke dalibai 18 kuma ana tsare da su a ofishin jami’an tsaron jami’ar cikin yanayi na akuba har zuwa wayewar garin Talata.

A lokacin mayarda martani Farfesa A. M. Gimba, da ke kula da harkokin ɗalibai ya ce ya yi gargadin cewa mahukunta makarantar za su dau matakai masu tsauri kan wadanda suka yi kokarin tada zaune tsaye a makarantar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here