Gwamnan Jahar Gombe ya Bawa Wanda ya yi Tattaki Saboda Buhari Kyautar Mota
Gwamna Muhammadu Yahaya na jihar Gombe, ya yi wa mutumin da ya yi tattaki saboda Buhari a 2015 kyautar mota.
A makon da ya gabata ne mutumin mai suna Dahiru Buba ya nemi a kawo masa doki shekaru biyar bayan ya yi tattaki daga Abuja zuwa Gombe.
Gwamnan ya ce ya yi umurnin daukar Buba a kai asibiti domin bashi cikakken kulawa Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya ya bai wa mutumin da ya yi tattaki daga Gombe zuwa Abuja domin murnar nasarar zaben Shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2015 kyautar mota.
Har ila yau, gwamnan ya bai wa mutumin mai suna Dahiru Buba Dukku zunzurutun kudi har naira miliyan biyu.
Read Also:
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga mai ba wa gwamnan shawara a kan kafofin watsa labarai, Ismal Uba Misili, sashin Hausa na BBC ta ruwaito.
A yanzu haka, Buba mai shekaru 50 na fama da matsalar ciwon kafa.
An kuma mika mashi kyautar ne a babbar birnin tarayya Abuja, a ranar Litinin, 16 ga watan Nuwamba.
A cewar sanarwar, gwamnan ya ba shi kyautar ne saboda tsananin kaunar da yake yi wa jam’iyyar APC mai mulki a kasar.