‘Yan Sanda Sun Kama Kasilan da ya yi wa Matar Dan Uwansa Duka

Ƴan sanda sun tsare Blackson Etche da ake zargi da yi wa matar yayansa, Love, duka.

Blackson ya amsa gayyatar da ƴan sanda suka yi masa inda suka tsare shi don cigaba da bincike.

Blackson ya musanta cewa ya doki matar yayansa, Love, don haka ƴan sanda suka bukaci a gayyato ƴan uwansa mata don su bada ba’asi Rundunar ƴan sandan Jihar Rivers ta ce ta kama Kansila a majalisar Etche, Blackson Nwanyawu kan zargin yi wa matar yayansa duka.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Nnamdi Omoni, ya sanar da wakilin The Punch a ranar Litinin cewa an tsare Blackson bayan ya kawo kansa ofishin ƴan sanda bayan gayyatarsa.

Tunda farko, Legit.ng ta ruwaito cewa wacce abin ya faru da ita, Love Nwanyawu, ta zargi Blackson, wanda shine shugaban majalisar Etche, da wasu mutane da yi mata rauni bayan zargin ta da

Love ta yi korafi game da lamarin a ofishin kare hakkin bil adama na rundunar ƴan sanda. Omoni, kansilar, ya musanta cewa ya yi wa matar dan uwansa duka. Ya ce, “Blackson yana tare da mu don amsa gayyatar mu.

Ya yi jawabi ya musanta cewa ya doki matar. Mun ce ya kira ƴan uwansa mata da suma an ambace su a cikin lamarin.

“Don haka, har yanzu muna kan bincike. Yana tsare muna masa tambayoyi. Ya musanta zargin, za muyi ƙoƙarin tabbatar da ingancin abinda muke zarginsa daga ƙarshe doka za tayi halinta.”

Omoni ya ce wacce abin ya faru da ita tana asibiti tana karɓar magani kuma muna kira ga dukkan iyalan su zauna lafiya su bari ƴan sanda ta yi bincike.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here