Aikin Hajji: Gwamnan Jahar Legas ya Shawarci Musulman Jaharsa

 

Babajide Sanwo-Olu, gwamnan Jihar Legas ya shawarci al’umma musulmi su rungumi tsarin tarin kudin hajji da jiharsa ta bullo da shi.

Sanwo Olu ya ce bayyana hakan ne a wurin kaddamar da sabon tsarin da hukumar aikin hajji na kasa ta tsara a jihar Legas.

Ya ce an yi tsarin ne musamman don mutane masu karamin karfe ta yadda za su iya tara kudin a hankali idan ya kai na kujera sai su tafi sauke faralin.

Gwamnan Jihar Legas, Mista Babajide Sanwo-Olu ya yi kira ga masu niyyar zuwa aikin hajji a jihar su rungumi sabon tsarin tara kudin kujerar hajji da jihar ta bullo da shi.

Sanarwar da aka fitar a ranar Litinin ta ce ya bada shawarar ne yayin rantsar da tsarin a Eko FM Marwquee, da ke LTV Complex, Agidingbi, Ikeja a Legas, The Punch ta ruwaito.

Gwamnan wadda ya samu wakilcin mataimakinsa, Dakta Obafemi Hamzat, ya ce wannan tsarin da hukumar aikin hajji na kasa ta shirya zai bawa marasa karfi ikon tara kudi a lokaci mai tsawo har ya kai adadin da zai basu ikon zuwa kasa mai tsarki sauke farali.

Ya ce sabon tsarin abin maraba ne musamman a wannan lokacin da karyewar tattalin arzikin duniya ya shafi kowa.

Sanwo Olu ya kuma yi kir ga dukkan mutane su kare kansu daga annobar COVID 19.

“Har yanzu cutar tana nan kuma tana yaduwa. Ya zama dole mu san matsayin mu kuma mu rika bin dokokin da aka gindaya na bada tazara, wanke hannu da ruwa da sabulu, amfani da hand sanitiza da saka takunkumin rufe fuska. Kazalika, mu guji rungumar juna, yin hannu da taron mutane da yawa,” ya kara da cewa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here