Lai mohammed

Gwamnati na Cigaba da Ragargazar ‘Yan Ta’adda da Masu Tada Kayan Baya Domin Samar da Tsaro a Kasar – Lai Mohammed

 

Lai Mohammmed, Ministan Labarai da Al’adu ya ce gwamnatin tarayya na cigaba da ragargazan yan bindiga ne don samar da tsaro a kasar.

Mohammed ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labarai a Calabar, babban birnin Jihar Cross Rivers.

Ministan Labaran ya bawa yan Najeriya tabbacin cewa matsalar rashin tsaro na daf da zama tarihi musamman idan aka kwantanta 2015 da 2022.

Cross Rivers – Ministan Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce gwamnati na cigaba da ragargazar yan ta’adda da masu tada kayan baya domin samar da tsaro a kasar.

Ministan ya bayyana hakan ne a Calabar yayin taron manema labarai tare da Gwamnan Cross River, Farfesa Ben Ayade, yayin bikin ranar yawon bude ido na duniya ta shekarar 2022.

Ya ce ana bukatar ayyukan gine-gine da tsaro kafin yawon bude idanu ya bunkasa, Vanguard ta rahoto.

Alhaji Mohammed ya ce:

“Zan iya bugun kirji a nan in ce cikin watanni uku da suka gabata, har masu sukar mu za su yarda cewa gwamnati ta fara samun nasara wurin samar da tsaro. A bangaren rashin tsaro, ina son tabbatar muku cewa abu mafi muni ya wuce.”

Ya ce idan aka kwatanta halin da kasar ke ciki a shekarar 2015 da yanzu a 2022, babu shakka akwai hujoji da ke goyon bayan matsayin gwamnati na cewa ana samun cigaba.

Ministan ya ce:

“Abin takaici ne ganin mutanen da ke tsokaci kan rashin tsaro ba su duba halin da muke a 2015 da halin da muke a yanzu.

“A 2015, dukkan yankin arewa maso gabas ba wurin zuwa bane. Da aka nada ni Minista a 2015, daya cikin ayyukan da na fara shine zuwa arewa maso gabas, musamman Maiduguri, Kaure, Konduga da Bama tare da tawagar yan jarida na gida da kasar waje don ganin barnar da yan Boko Haram suka yi.

“A ranar 5 ga watan Disamban 2015 muka tafi kuma sai da jiragen sojojin sama suka mana rakiya daga Maiduguri zuwa Bama, nisar kilomita 68 tsakaninsu. Baya ga ayyarin motoccin mu, ba mu ga wasu motocci ba. Boko Haram sun lalata dukkan gidajen da ke Bama. Babu makarantu da asibitoci a arewa maso gabas. An lalata layyukan sadarwa.”

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here