An Gano Maboyar ‘Yan Bindiga a Kaduna, An Ceto Mutane 3 da Suka Sace

 

‘Yan bindiga sun sha ragargaza a hannun sojojin Najeriya yayin da aka gani maboyarsu a jihar Kaduna.

An ceto mutum uku da tsageru suka sace, an kuma mika su ga danginsu jim kadan bayan bincike a kansu.

An kuma kwato wasu makamai da kayayyakin aikata laifuka a maboyar ‘yan ta’adda bayan share ta.

Kaduna – Jami’an sojin rundunar Operation Forest Sanity sun farmaki maboyar ‘yan bindiga a kokarin da suke na kakkabe dazukan Kuriga-Manini-Udawa a hanyar Chikun zuwa Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaron jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yau Laraba 28 ga watan Satumbam Leadership ta ruwaito.

Aruwan ya ce, jami’an tsaron sun yi arba da ‘yan bindigan, kuma sun tsere da raunukan harbin bindiga yayin da sojoji suka fi karfinsu.

Sanarwar ta kuma kara da cewa, an kwato bindiga kirar AK-47, harsasai 18 da kuma wasu makamai 11.

A cewar sanarwar:

“A farmakin da aka kai maboyar, rundunar tsaro ta ceto mutum uku da aka yi garkuwa dasu, sune; Luka Ibrahim, Yusuf Jibril da Saminu Abdullahi.”

Ta kuma kara da cewa, gwamnatin jihar Kaduna ta yaba da kwazon soji bisa wannan nasara da suka samu na fattakar ‘yan bindiga, haka nan Daily Sun ta ruwaito.

Aruwan ya kara da cewa:

“Wadanda aka ceton tuni an hada su da ahalinsu. Dakaru za su ci gaba da aiki tukuru a dukkan yankunan.” Hakazalika, ya kuma nemi mazauna jihar da su sanar da jami’an tsaro duk wani motsin ‘yan ta’adda wadannan lambobin wayan: 9034000060 da 08170189999.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here