Ban ga Dalilin da Zai sa Gwamnati ta ki Yin Sulhu da ‘Yan Bindigan da Suka Nuna Sha’awar Yin Sulhu ba – Sheikh Gumi

 

Sheikh Ahmad Gumi ya ce yan bindiga ba za su mika wuya ba sai sun tabbatar ba abinda zai same su.

Gumi ya kuma ce bai ga dalilin da zai sa gwamnati ta ki yin sulhu da yan bindigan da suka nuna sha’awar yin sulhun ba.

Babban malamin ya yi wannan jawabin ne yayin wani taron da aka yi kan kallaubalen tsaro da ke adabar Nigeria Sheikh Ahmad Gumi, shahararren malamin addinin musulunci ya ce yan bindiga ba za su ajiye makamansu ba har sai an basu tabbacin babu abinda zai same su sannan za a taimaka musu.

Gumi ya yi wannan furucin ne a ranar Laraba yayin wani taro da aka yi ta yanar gizo da Cibiyar Nazarin Dokoki Da Demokradiyya ta shirya, The Cable ta ruwaito.

An shirya taron ne ne domin tattaunawa a kan kallubalen tsaro da ke adabar sassan Nigeria da dama.

Malamin ya ce bai ga dalilin da zai sa gwamnati ba za ta yi sulhu da yan bindigan da suka amince suna son a yi sulhun ba. Gumi ya ce, “Babu wanda zai iya hallasta laifi, abinda muka gani shine yakin kabilanci tsakanin wadanda ke daji da mutanen kauyen da ke makwabtaka da su.

A lokacin da makiyayi ke da matsalaloli, babu wanda ya kula shi don haka ya dauki makami. “Da muka tafi can suka ga akwai wanda zai saurare su, sun shirya yin sulhu, sun fada mana matsalolinsu kuma a shirye suke so koma cikin gari.

A wannan halin, ban ga dalilin da yasa gwamnati ba za ta yi sulhu da su ba.”

Gumi ya ce idan ba a nuna musu cewa babu abinda zai same su ba idan sun koma cikin mutane, ba za su ajiye makamansu ba.

Malamin addinin ya ce a yi musu afuwa kamar yadda aka yi wa tsagerun Neja Delta.

“Idan ba a nuna musu cewa babu abinda zai same su ba idan sun koma cikin gari, ba za su bar makamansu. Hakan yasa na nemi a musu afuwa kamar yadda aka yi wa yan Niger Delta. “Ba laifi na ke hallastawa ba, abinda suka yi laifi ne.

Amma suna garkuwa da mutane ne domin samun kudi su sake siyan makamai su kare kansu.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here