Gwamnatin ƙasar Mali ta Kori Jami’in Majalisar Ɗinkin Duniya

 

Gwamnatin mulkin soji ta ƙasar Mali ta bai wa shugaban dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya wa’adin kwana biyu ya fice daga ƙasar.

A wata sanarwar da aka karanta a kafar talabijin ta gwamnatin ƙasar, mai magana da yawun gwamnatin ƙasar ya ce shugaban dakarun, Guillaume Ngefa-Atondoko Andali ya aikata ayyuka na zagon-ƙasa a wajen zaɓen shaidun da aka gabatar domin yin bayani a gaban kwamityin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya.

A watan jiya, wani mai hanƙoro na wata ƙungiyar fararen hula wanda ya yi bayani a zauren kwamitin tsaron na MDD, ya yi zargin cewa ana take hakkin bil’adama ƙarƙashin ayyukan soji na haɗin gwiwa da Mali ɗin ke yi da Rasha.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here