Jonathan: Gwamnonin APC Sun Nuna Gazawa
Ziyarar da gwamnonin APC suka kaiwa tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan na ci gaba da haifar da cece-kuce.
PDP a martaninta ga ziyarar na gwamnonin APC ta bayyana shi a matsayin lamuncewa adawa.
Kakakin jam’iyyar, Ologbondiyan ya ce ziyarar ya kuma tabbatar da cewar Najeriya ta fi inganta a karkashin shugabancin PDP.
Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana cewa ziyarar da gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) suka kaiwa tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kara tabbatar da cewar Najeriya ta fi inganta a karkashin mulkinta.
Read Also:
Legit.ng ta tattaro cewa PDP ta bayyana hakan ne yayinda take martani ga ziyarar da gwamnan suka kai a ranar Juma’a, 20 ga watan Nuwamba, inda ta bayyana hakan a matsayin lamuncewa mulkin jam’iyyar adawar.
Gwamnonin APC karkashin jagorancin Shugaban jam’iyyar kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni sun gudanar da wani taron sirri tare da Jonathan a gidansa da ke Abuja.
Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, 22 ga watan Nuwamba, ta kakakinta, Kola Ologbondiyan.
A cewar Ologbodinyan, jam’iyyar adawar ta amshi ziyarar na gwamnonin APC a matsayin ban hakuri daga jam’iyya mai mulki zuwa PDP da yan Najeriya a kan karairayi da sauran zarge-zarge da aka yi amfani da su don karbar mulki.
Ologbodiyan ya kuma gargadi yan Najeriya a kan su yi taka-tsantsan da dabarun APC, cewa jam’iyyar ba za ta bari gajiyayyar jam’iyyar da makiranta su sake batar dasu ba.