Mutanen Habasha 11 Sun Mutu a Hatsarin Mota a Somalia

 

Mata shi da maza biyar ‘yan asalin Habasha sun mutu a wani hatsarin mota da ya ritsa da su a Somalia, In ji hukumar kula da ‘yan cirani ta duniya.

Rahotanni sun ce masu safarar mutane ne suka shirya shigar da su Yemen ta tashar ruwan Bosasom in ji IOM.

Amma motar da ke ɗauke da su ta faɗi ne a ranar Talata, lokacin da ta kusa kaiwa ga tashar ta Bosaso. kamar yadda IOM ta bayyana.

Ana ci gaba da bincike kan yadda lamarin ya faru, sai dai wasu na cewa wataƙila motar tasu ce ke da matsala, saboda ba a ga wani abun hawa da suka yi hadarin ba tare.

An tabbatar da an binne gawa 11. akwai kuma aƙalla mutum 20 da suka jikkata a motar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com