Sudan: Ƙasa ta Rufta Kan Masu Haƙar Ma’adanai

Aƙalla masu haƙar ma’adanai 10 ne suka mutu a wani hatsari da ya rutsa da su a arewacin Sudan, wasu mutum 20 na daban suka jikkata.

Kafaffen yaɗa labarai na cikin gida sun ɗora alhakin faruwar hakan kan ruftawar ƙasa wajen yaƙar da ake yi da manyan injina.

Irin waɗannan lamura ba baƙi ba ne a harkokin ma’adanai a Sudan.

Wata shida da suka gabata, mutum 11 sun mutu a irin wannan lamari kuma yankin arewacin Sudan din, yayin da ake samun rahotanni marasa dadi irin waɗannan a yammacin Darfur da kudancin Kordofan.

An yi amannar cewa mutum miliyan biyu ne ke aiki a yankin da ake haƙar ma’adanai a Sudan.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com