Dukkanin Hallitun Ruwa na Fuskantar Haɗarin Guba da Yunwa da Rashin iska -MDD
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa ana samun matukar karuwa a yawan robobin da ke gurɓata muhalli a cikin teku waɗanda ke haifar da babbar barazana ga lafiyar ɗan Adam da hallitun ruwa da kuma tattalin arziki.
Read Also:
Wani rahoto na hukumar kula da muhali ta MDD ya ce yawan robobin da ke cikin teku zai ninka sau uku nan da shekarar 2040.
Ya ce dukkanin hallitun ruwa na fuskantar haɗarin guba da yunwa da rashin iska.
Rahoton ya kuma ce ana bukatar ɗaukar mataki cikin gaggawa domin rage yawan robobin da ake amfani da su amma shugabbanin ba su da kudirin yin haka.