MDD za ta Kafa Asusu na Musaman Don Taimakawa Afghanistan  

 

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta kafa asusu na musaman dan samar da tsabar kudi da ake bukata cikin gaggawa ga yan Afghanistan bayan da Taliban ta karbe iko a watan Augustan daya gabata.

Shugaban hukumar raya kasa ta MDD, Achim Steiner ya ce ya yinda tattalin kasar ke fuskantar koma baya, manufar shirin it ace ta taimaka wa yan Afghanistan yadda za su yi rayuwa a lokacin sanyi.

Ya ce abin da muke gani shi ne bayan matsalar rikicin siyasa da kasar ta ke fusknta tana kuma fuskantar matsalar durkushewar tttalin arziki.

Mista Steiner ya kuma ce Jamus ce kasa ta farko da ta yi alkawarin bayar da gudummawar dala miliyan 58 ga sabon asusun.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here