Tanzania ta Hana Ajiye Gumaka Masu Tsiraici na Tallata Kaya a ƙofar Shaguna

 

Hukumomi a wani lardin ƙasar Tanzaniya sun hana ‘yan kasuwa ko teloli ajiye irin gunkin nan na tallata tufafi da sauran kayan sanya wa, wanda ba a rufe jikinsa ba sosai, inda za a iya ganin wani sashe na jiki kamar nono, a ƙofar shagunansu.

Shugaban al’ummar garin Unguja a yankin tsibirin Zanzibar, Rashid Msaraka, ya ce an ɓullo da dokar ne domin kare al’adu da kimar ƙasar.

A wata hira da ya yi da wata kafar yaɗa labarai ta intanet a ƙasar ta gabashin Afirka Mr Msaraka ya ce masu irin waɗannan kasuwanci da ke buƙatar tallata kayansu da irin waɗannan gumaka za su iya ajiye su a cikin shagunansu.

Ya ce irin waɗannan gumaka da ba a sanya musu kaya sosai, ta yadda za ka iya ganin kamar nonon mace, haɗari ne ga yara ‘yan makaranta da matasa da ke wuce su a ƙofar shaguna.

Shugaban ya ce sun samu ƙorafi ne daga jama’a da ke fargabar illar gumakan ga tunani da halayyar mutane musamman matasa.

Ya ƙara da cewa ya san wasu yankunan ƙasar suma za su biyo sahu wajen yin dokar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here