Bani da Hannu a Raba Kwangiloli a Tsohuwar Gwamnatin Mahaifina – Bello El-Rufai

 

Bello El-Rufai ya bayyana cewa babu hannunsa ko kaɗan a raba kwangiloli a tsohuwar gwamnatin Kaduna karkashin mahaifinsa.

Ɗan majalisar tarayya ya ce tsohon gwamna, Malam Nasir El-Rufai mutumin kirki ne wanda Najeriya ke buƙata a matsayin shugaba.

Ya ce da shi aka yi kamfe a lokacin da mahaifinsa ke neman zama gwamnan Kaduna amma bayan an ci zaɓe aka nesanta shi da gwamnati.

Kaduna – Ɗan majalisa mai wakiltar Kaduna ta Arewa a majalisar wakilan tarayya, Bello El-Rufai’i ya ce bai taɓa karɓan kwangila a mulkin mahaifinsa ba.

Bello, ɗan tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai,ya ce ba ruwansa da harkokkn ba da kwangila a tsohuwar gwamnatin da ta gabata a jihar Kaduna.

Ɗan majalisar tarayyar ya bayyana haka ne a wata hira da Yaya Abba ya shirya mai taken ‘Tare da Shuraim’, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Muƙaman da El-Rufai ya riƙe

Malam Nasir El-Rufai ya rike mukamin ministan babban birnin tarayya daga shekarar 2003 zuwa 2007 a karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Bayan haka, ya zama gwamnan jihar Kaduna na tsawon zango biyu daga 2015 zuwa 2023, rahoton Naija News.

Kwanan nan aka zarge shi da bar wa magajinsa, Malam Uba Sani tulin bashi da ya kai Dala miliyan 587, N85bn, da kuma N115bn na kwangila.

Gwamna Uba Sani ya ce bashi ya yi wa Kaduna katutu kuma ƴan kuɗaɗen shigar da take samu kaɗai ba su kai a biya ma’aikata albashi ba.

Shin ana baiwa Bello kwangila a mulkin mahaifinsa?

Da yake jawabi, Bello El-Rufai ya ce:

“Ina ganin shi (Malam Nasir) mutum ne na kwarai kuma irin shugaban da Nijeriya ke bukata, akwai mutane da yawa kamarsa. Mun masa kamfe sosai.

“Amma yana zama gwamna ya tura ni gefe, kamar yadda na ce, na yi hijira. Ba kamar ’ya’yan gwamnoni a lokacin ba, a gaskiya ban zauna a Kaduna ina yin kwangiloli ba.”

Yayin da yake bayyana cewa yanzu ya fahimci dalilin da ya sa mahaifinsa ya yanke shawarar tsame shi daga fagen siyasa a lokacin, Bello ya ce:

“Abin da ke faruwa da wanda ke kan mulki shi ne idan suka gaza tunkararsa kai tsaye, sai su lallaɓa wurin matansa ko ƴaƴansa. Haka ƴan kwangila suke a Kaduna, suna tunanin idan suna bi ta hannunka za a masu alfarma.”

“Ya tsame ni gaba ɗaya daga lissafin mulki kuma hakan ya taimaka sosai.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Logged in as Khadija Garba. Log out?

Please enter your comment!