Sabuwar Hanyar da Za’a Kawo Karshen Rashin Tsaro a Zamfara – IGP Usman Baba
Sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya, IGP Usman Baba, ya kawo sabuwar hanyar kawo karshen rashin tsaro a jahar Zamfara.
Mataimakinsa, AIG Zone 10 na Sokoto, Ali Janga ne ya bayyana hakan a ranar Laraba lokacin da ya kai ziyara Zamfara a kan matsalar rashin tsaro.
A cewarsa, IGP ne ya umarce shi da ya zauna da jami’an tsaro don su tattauna akan ayyukan dan sanda akan harkar tsaron kasa.
Zamfara – Sifeta janar na ‘yan sanda, IGP, Usman Baba ya kawo sabuwar hanyar kawo karshen rashin tsaron da jahar Zamfara take fuskanta.
Read Also:
AIG na Zone 10 na jahar Sokoto, Ali Janga ne ya bayyana hakan a ranar Laraba lokacin da ya kai ziyara a kan wannan rashin tsaron da jahar ta ke fuskanta, Daily Nigerian ta rawaito.
Yayin tattaunawa da manema labarai bayan wani taro da ‘yan sanda da yayi a Gusau, AIG ya ce IGP ya sauya hanyar kawo karshen rashin tsaron da jahar Zamfara da sauran jahohi suke fuskanta.
Na zo nan bisa umarnin IG don in tattauna da jami’an hukumar dan sanda a kan ayyukansu.
Mun samu wata sabuwar hanyar gyara tsaro a jahar. Za mu hada kai ne da sauran jami’an tsaron wasu jahohi don kawo karshen rashin tsaron da ake fuskanta,”cewar Janga.
Daily Nigerian ta wallafa cewa, AIG ya umarci jami’an hukumarsu da su kasance masu kwazo da dagiya sannan su zama cikin shiri a ko yaushe.
AIG ya kai wa sarkin Gusau ziyara, Alhaji Ibrahim Bello, inda ya nemi goyon bayan shugabannin gargajiya wurin kawo karshen ‘yan bindiga a jahar.