Shugaba Buhari ya Umarci Shugabannin Tsaro da su Nemo Hanyoyin Magance ƙalubalen Tsaro

 

Shugaba Buhari ya umarci shugabannin tsaron ƙasar nan su nemo hanyoyi da dabarun magance ƙalubalen tsaro.

Shugaban ya sabunta wannan umarnin yayin taronsa da shugabannin tsaron yau a fadarsa dake Abuja.

Ministan Tsaro, Bashir Magashi, yace ragowar jiragen yakin da gwamnati ta siyo daga Amurka zasu iso Najeriya mako mai zuwa.

Abuja – Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya umarci shugabannin tsaro su gaggauta nemo hanyoyin warware ƙalubalen tsaro da ya addabi ƙasar nan, musamman a arewa maso yamma da arewa maso tsakiya.

Channels TV ta rahoto cewa Buhari ya bada wannan umarnin ne a fadarsa dake Abuja, yayin taronsa da shugabannin tsaro, wanda ya shafe awanni biyar ranar Talata.

Shugaban ya jaddada bukatar dakile ayyukan yan bindiga, waɗanda a cewar shugabannin tsaron suna kashe al’umma da sace su domin jawo hankalin duniya.

Wane abubuwa aka tattauna a wurin taron?

Ministan tsaro, Janar Bashir Magashi, ya shaidawa manema labaran gidan gwamnati bayan taron cewa gwamnati ta sake nazari kan yanayin da ƙasa ke ciki.

A cewar Magashi taron ya cimma matsaya cewa za’a nemo hanyoyin magance duk wani ƙalubalen tsaro musamman a Zamfara da arewa ta tsakiya, wanda taron ya maida hankali a kai.

Bugu da kari ministan ya bayyana cewa gwamnati zata samu nasarar cimma waɗannan muradan ne idan yan Najeriya sun bata haɗin kai.

A cewar Magashi taron ya cimma matsaya cewa za’a nemo hanyoyin magance duk wani ƙalubalen tsaro musamman a Zamfara da arewa ta tsakiya, wanda taron ya maida hankali a kai.

Bugu da kari ministan ya bayyana cewa gwamnati zata samu nasarar cimma waɗannan muradan ne idan yan Najeriya sun bata haɗin kai.

Mako mai zuwa sabbin jiragen yaƙi zasu kariso

Magashi ya ƙara da cewa mako mai zuwa rukuni na biyu na jiragen yaƙin A – 29 Super Tucano zasu ƙariso Najeriya, yayin da aka fara gwajin jiragen da suka iso a rukunin farko.

Taron tsaron da ya gudana yau, ya samu jagorancin shugaban ƙasa Buhari, inda baki ɗaya shugabannin tsaro suka halarta.

Hakanan kuma shugabannin tsaron bisa jagorancin shugaban jami’an tsaro, Manjo Janar Lucky Irabor, da ministan tsaro, Janar Bashir Magashi.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai sufeto janar na yan sanda, Usman Baba, Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, da ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here