An Kai Hari Ofishin Jakadancin Saudiyya Dake Hague

 

Hukumar yan sanda dake Hague, kasar Netherlands a ranar Alhamis, 11 ga Nuwamba, ta tabbatar da labarin cewa an yi harbe-harbe a ofishin jakadancin kasar Saudiyya.

Bayan samun labarin harbe-harben, jami’an tsaron garin inda kotun duniya ICC take sun garzaya cikin ginin kuma sun samu harsasai a kasa, tashar ABC News ta ruwaito.

Amma, a cewar kakakin hukumar yan sanda dake Hague, Steven van Santen, babu wanda aka kashe ko ya ji rauni.

Har yanzu, yan sanda basu san dalilin da yasa aka kai hari ofishin jakadancin Saudiyya ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here