Rundunar Sojoji ta Koka da Maciya Amanan Cikin ta

Rundunar sojoji ta ce kalubalen tsaro a yankin arewa na neman fin karfin gwamnatin Najeriya.

A cewar rundunar sojoji, hatta a cikin sojoji akwai maciya amana.

A ranar Laraba ne sakataren gwamnatin kasar Amurka ya ce Amurka za ta taimakawa Najeriya ta fatattaki ‘yan ta’adda Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa karfin sojoji kadai ba zai kawo karshen kalubalen tsaro da yankin arewa maso yamma da sauran sassan kasa ke fama da shi ba, tare da sanar da cewa “hatta a cikin sojoji akwai maciya amana”.

An fadi hakan ne yayin wani taro da rundunar soji ta yi da manema labarai daga Katsina da Zamfara wanda aka yi a sansanin sojoji na musamman da ke Faskari a jihar Katsina.

Rundunar sojin ta jaddada muhimmancin hada karfi da karfe a tsakanin hukumomin tsaro da sauran jama’ar farar hula domin samun zaman lafiya mai dorewa.

“Mun gaji da duk wannan zargi da jama’a ke yi wa rundunar sojoji a kan cewa su na kallo ‘yan bindiga ke cin karensu babu babbaka a yankin arewa maso yamma ba tare da yin komai a kan hakan ba,” kamar yadda jami’in sojoji ya koka.

“Hatta a cikin sojoji akwai maciya amana, shi yasa makiyanmu, ‘yan bindiga, ke samun wasu muhimman bayanai” Jami’in ya ce rundunar sojoji ba ta tare da ‘yan bindiga kuma za ta cigaba da yakarsu.

A cewar jami’in, jama’a su cigaba da taya rundunar soji da addu’a saboda batun tabarbarewar tsaro na neman ya fi karfin Najeriya.

Kazalika, ya bukaci jama’a su gaggauta bawa hukumomin tsaro goyon baya ta hanyar basu muhimmman bayanan da zasu kai ga kama ‘yan bindiga tare da dawo da zaman lafiya a yankin arewa maso yamma.

Ya kara da cewa rundunar soji za ta adana sirrin duk wanda ya bata bayanai, a saboda haka kar jama’a su ji tsoro.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here