Tsohon Shugaban Kasan Ghana, Jerry Rawlings ya Mutu

 

Shahrarren tsohon shugaban kasar Ghana, Jerry Rawlings, ya mutu bayan kamuwa da cutar COVID-19.

TheCable ta tattaro cewa tsohon shugaban kasan ya mutu ne a asibitin Korle-Bu dake Accra, babbar birnin kasar, da safiya Alhamis.

Rawlings, wanda tsohon shugaban mulkin Soja ne ya yi mulkin Ghana tsakanin 1981 da 2001.

Ya kasance shugaban kasa karkashin mulkin Soja zuwa 1992, sannan ya koma demokradiyya kuma yayi mulki zuwa 2001.

A matsayinsa na hafsa a hukumar Sojin saman Ghana, Rawlings yayi kokarin juyin mulki a Mayun 15, 1979, amma bai samu nasara ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here