Hasashen Bankin Duniya ya Nuna Tsawon Shekarun da Matsin Tattalin Arziki Zai Kai

 

Masanan Bankin Duniya sun fadi abin da zai faru da tattalin arzikin Najeriya.

World Bank Nigeria Development Update ta ce babu tabbacin za a tsira a 2022.

Yawan Talakawa zasu karu da miliyan 20, kuma za a iya yin yunwa nan gaba.

Babban bankin Duniya ya yi wa Najeriya hasashen shekaru uku a cikin matsin lambar tattalin arziki muddin ba a dauki matakan da su ka dace ba.

Jaridar Daily Trust ta rahoto bankin Duniya ya na cewa muddin ba a cigaba da tafiya a kan dabarun ceto kasar ba, Najeriya za ta dade a matsala.

‘Nan da shekaru uku, akasarin ‘Dan Najeriya na iya ganin ci-bayan nasarorin cigaban tattalin da aka samu na shekaru, kuma kasar na iya fada wa cikin matsin da ya fi kowane tun 1980s.”

Jawabin da World Bank Nigeria Development Update (NDU) ta fitar dazu ya bayyana wannan.

A cewar World Bank Nigeria Development Update, kasar na iya guje wa wannan matsala idan aka dage wajen bin manufofi da tafarkin da su ka dace.

An fitar da wannan bayani ne da taken: “Rising to the Challenge: Nigeria’s COVID-19 response”.

Darektan babban bankin Duniya a Najeriya, Shubham Chaudhuri ya ce kasar tana cikin gaba mai wuya na daukar matakin da zai kai ta ga ci ko akasin haka.

“Babu tabbacin dawowa daidai a 2021, kuma hakan ya danganta da matakan da aka dauka.” Chaudhuri ya ce kila Talakawa su karu da miliyan 20 a 2022.

Hasashen yace za ayi fama da karancin abinci a lokacin da ake fuskantar annobar COVID-19 da karyewar farashin gangar danyen mai a kasuwannin Duniya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here