Rikici ya Barke Tsakanin ‘Yan Sanda da Fusatatun Matasa

 

Duk da zanga-zangar EndSARS, wani dan sanda ya kuma kashe wani ba gaira ba dalili.

Rikici ya kaure a birnin Fatakwal ranar Alhamis sakamakon wannan kisa.

Abokan aikin direban sun dauki gawarsa kan titi suna zanga-zanga.

Rikici ya barke a unguwar Rokpoku na birnin Fatakwal sakamakon bindige direban a-daidaita-sahu (Keke Napep).

Wannan abu da ya faru misalin karfe 7 na safiya Alhamis, a hanyar tashar jirgin sama ya haddasa rikici a yankin.

Wasu fusatattun matasa da abokan direban sun toshe hanyar suna zanga-zanga. Wani mai idon shaida ya ce dan sandan ya kashe direban ne saboda ya ki bashi na goron N100 da ya bukata.

The Cable ta ce kakakin hukumar yan sandan jihar, Nnamdi Omooni, ya tabbatar da hakan nda yace an damke jami’in da yayi kisan.

“Ina sane da abinda ya faru a Rukpokwu. Daya daga cikin jami’anmu ya kashe wani matukin keke da safen nan.

An kwace makamin dan sandan kuma an tsareshi yanzu,” yace.

“Mun tura mazajenmu wajen domin kwantar da kuran da kuma hana barkewar rikici.”

“Muna kira ga mutane sun kwantar da hankulansu, su bari mu hukuntashi.”

“Kisan dans anda ko kona ofishin yan sanda ba zai dawo da wanda aka kashe ba; inamma hakan munanan abu zai yi.”

Wannan na zuwa watanni biyu bayan zanga-zangar EndSARS ta barke a Najeriya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here