Hatsaniya ta ɓarkewar a Kotun Sauraron ƙararrakin Zaɓen Shugaban ƙasa
An samu ɓarkewar hatsaniya a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa a ranar Laraba lokacin da ɓangarorin jam’iyyar Labour guda biyu suka far wa juna.
Hatsaniyar ta soma ne lokacin da shugaban jam’iyyar, Lamidi Apapa ya isa kotun tare da wasu magoya bayansa.
Read Also:
Apapa wanda ke takun-saka da shugaban jam’iyyar da aka dakatar, Julius Abure, ya isa kotun ne domin sauraron ƙarar da Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ta LP ya shigar, inda yake kalubalantar nasarar zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Hatsaniyar ta ɓarke ne a lokacin da ya yi kokarin zama a wurin da wakilan jam’iyyar Labour suke a cikin kotun.
Wani wakilin jam’iyyar ya tambayi Apapa “Waye kai?” inda ya mayar da martani da cewa, “Ba ka san ko ni waye ba? Kalli yanda kake magana, kai ma waye kai?”
Yayin da aka ci gaba da hatsaniyar, Apapa ya ɗaga murya tare da cewa, “Tashi, ba za ka zauna a nan ba”.
Sai dai sakatariyar kotun sauraron korafin zaɓen shugaban ƙasar, Josephine Ekperobe, ta yi sauri domin shiga tsakani da kuma daidaita al’amura.