Adadin Kudin da Muke Buƙatar Domin Kai Kayan Agaji Sudan – MDD

 

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce tana buƙatar $3bn domin kai agaji zuwa Sudan.

MDD ta ce ana sa ran mutum sama da rabin miliyan ne za su tsere daga ƙasar a daidai lokacin da ake ci gaba da faɗa tsakanin sojojin gwamnati da kuma dakarun RSF.

Jagoran ɓangaren ayyukan jin kai na MDD, Ramesh Rajasingham, ya ce mutum sama da rabi na al’ummar Sudan miliyan 25 – na buƙatar agaji da kuma kariya.

Ya ce wannan shi ne alkaluma mafi girma da aka taɓa gani a ƙasar.

Hanyar kai kayan agaji ita ce babbar matsala a yanzu.

An sace kayan abinci da aka kai ƙasar da kuma far wa ma’aikatan agaji tun bayan ɓarkewar faɗa tsawon wata ɗaya da ya gabata.

guest posting seo

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here