Shugaba Buhari ya Yaba wa Hilda Baci, da ke Kokarin Kafa Tarihin Girki a Duniya

 

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya yaba wa Hilda Baci da ke kokarin kafa tarihi a matsayin wacce ta fi daɗewa tana girki a duniya.

Buhari ya ce wannan abin alfahari ne ga ‘yan Najeriya kuma kowa ya yaba da jajircewa da Hilda ta nuna.

Wannan bajinta na Hilda na ci gaba da jan hankali a ciki da wajen Najeriya.

Har yanzu dai Hilda ba ta tsayar da girki ba duk da ta shafe sa’o’i 88. Burinta shi ne ta kafa tarihin da ba a taba yi ba a duniya.

Shugaba Buhari na fatan hakan ya kwaɗaita wa sauran matasa wajen cimma muradunsu na rayuwa.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here