Cin Zarafin ɗan Sanda: Rundunar Ƴan Sanda ta Tsare mawaki, Seun Kuti

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a Legas ta ce ta kama mawaki, Seun Kuti bisa zargin cin zarafin wani jami’in ɗan sanda.

Kakakin rundunar, Benjamin Hundeyin ya wallafa hoton mawakin a shafinsa na Twitter sanye da ankwa.

Kuti, wanda ɗa ne ga shahararren mawaƙi, marigayi Fela Kuti, ya miƙa kansa ne a shalkwatar ƴan sanda a Legas bayan da sufeton ‘yan sanda Usman Alkali Baba ya bayar da umurnin a kama shi.

An ga “wani bidiyon mawakin yana marin dan sanda sanye da kayan sarki”, in ji Kakakin ‘yan sanda.

Seun – ya miƙa kansa ne tare da rakiyar lauyansa a ranar Litinin.

Kafin a tsare shi, Kuti ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa ɗan sandan ya yi kokarin kashe shi tare da iyalansa, amma babu wani karin bayani.

Kawo yanzu Seun da lauyansa ba su mayar da martani ba a kan tsare shi.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here