Hauhawar Farashin Kayayyaki Matsala ce ta Duniya Baki ɗaya ba wai iya Najeriya ba – Garba Shehu
Mai magana da yawun shugaba Buhari, Garba Shehu ya ce hauhawar farashin kayayyaki matsala ce ta shafi duniya ba wai iya Najeriya ba.
Ya kuma bayyana cewa dogaron da Najeriya ta yi na shigo da komai daga ƙasashen waje ya ƙara taimakawa wajen tashin farashin.
Gwamnatin Buhari ta ce tana iya bakin ƙoƙarinta wajen ɗaukar matakan shawo kan hauhawar farashin kayayyakin.
Abuja – Mai magana da yawun shugaban ƙasa Malam Garba Shehu, ya ce hauhawar farashin kayayyaki matsala ce ta duniya baki ɗaya ba wai iya Najeriya ba.
A ranar Litinin ɗin nan ne hukumar ƙididdiga ta ƙasa wato NBS, ta fitar da rahoto wanda ke bayani akan ma’aunin farashin kayayyakin masarufi wato CPI.
CPI na auna hawa da saukar farashin kayayyakin da ake amfani da su a yau da kullum.
The Cable ta ce an samu hawan farashin kayayyaki daga 22.04% zuwa 22.22% a tsakanin watan Afrilu zuwa Mayun 2023.
NBS ta ce hauhawar da aka samu a watan Afrilu na da alaƙa da yadda aka yi ta samun hawan farashin a kowane wata tun daga farkon shekarar da muke ciki zuwa yanzu.
NBS ta ƙara da cewa kayayyaki irin su abinci, abubuwan sha, gidaje, ruwa, wutar lantarki, iskar gas, man fetur da sauran su ne suka ɗaga matsayin CPI ɗin.
Annobar Corona ce ta jawo rugujewar tattalin arziƙi
Biyo bayan wannan sanarwar ta NBS, wasu sun riƙa danganta hauhawar farashin kayayyakin da mulkin shekaru takwas na gwamnatin shugaban Buhari.
Sai dai, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Garba Shehu ya ce annobar COVID-19 ce ta jawo koma bayan tattalin arzikin duniya kuma babu wata ƙasa da abun bai shafa ba.
Ya ƙara da cewa dogaran da Najeriya ta yi na shigo da kayayyaki daga ƙasashen waje ya ƙara dagula al’amuran.
A kalamansa:
Read Also:
“An samu hauhawar faraashin kayayyaki a ko’ina ta dalilin kullen COVID-19, wanda hakan ya shafi tattalin arziƙin ƙasashe saboda rufe masana’antu da hanyoyin sufuri da aka yi.
“Wannan shi ne ya haifar da ƙarancin kayayyakin da kuma sabbaba hauhawar farashinsu a yayin da suka isa kasuwa” Mun dogara da kayan waje Ya kara da cewa, dogara da kayan kasashen waje na daga cikin matsalolin da Najeriya ke fuskanta wajen tashin kayayyakin cikin gida.
Ya kara da cewa:
“Duba da cewa Najeriya ta dogara kacokan kan shigo da kayayyaki masu muhimmanci irinsu man fetur, man girki, taki, sinadarai na amfanin gona, da sauran su, hauhawar farashin kayayyaki na duniya yakan yi tasiri sosai kan farashinmu na gida.
“Gwamnati, idan ba wai za ta zabi yin watsi da ƙa’idojin ciniki mara shinge bane, babu wani abinda za ta iya taɓukawa kan hakan.”
Yadda farashi ya shafi tattalin arziki Faransa, ta bakin Garba Shehu
Shehu ya bada misali da ƙasar Faransa, wacce ta sami daidaito kan hauhawar farashin kayayyaki na 4.1% cikin 100% daga 1960 zuwa 2022, a yau tana fama da hauhawar farashin da ya kai 1,080.36%.
Ya ƙara da cewa ƙasar Burtaniya ma na fama da hauhawar farashin da ya kai 10.1%. Na ƙasar Ghana kuma ya kai 54.1% na tsawon shekaru 20 kafin saukar da ya ɗan yi a kwankin nan. Adadin na Turkiyya ya kai 45%.
Yaƙin Ukraine ya ƙara dagula al’amuran
Garba Shehu ya ƙara da cewar yaƙin da ake yi a Ukraine ya ƙara sabbaba tashin gwauron zabon farashin kayayyakin abinci, wanda a dalilin haka ake fargabar karuwar yunwa a ƙasashe da dama.
Ya kuma ce abin damuwa ne yadda wasu ke ganin cewa kamar gwamnatin Buhari ba ta ƙoƙarin magance matsalar hauhawar farashin kayayyakin, rahoton Daily Post.
Ya ƙara da cewa Buhari ya na iya bakin kokarinsa, wajen shawo kan matsalar hauhawar farashin kayayyaki, kuma zai ci-gaba da yin hakan.