Jawabin Kwankwaso Bayan Ganawarsa da Tinubu

Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce tabbas ya gana da zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a Faransa.

Kwankwaso, jagoran NNPP mai kayan marmari, ya ce zai fitar da cikakken bayani kan tattaunawar ranar Alhamis .

Ana ganin wannan zama na manyan yan siyasan biyu ka iya jawo Kwankwaso zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaben 2023 karkashin inuwar jam’iyyar NNPP mai kayan marmari, Rabiu Kwankwaso, ya tabbatar da rahoton cewa ya gana da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu.

A wata hira da kafar watsa labarai TRT Afrika, tsohon gwamnan Kano, Kwankwaso, ya ce ba zai bayyana abinda suka tattauna ba sai ranar Alhamis mai zuwa.

Idan baku manta ba, shugaban Najeriya mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya gana da Kwankwaso, jagoran NNPP da kuma tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi a ƙasar Faransa ranar Talata.

Takaitacciyar hira da Kwankwaso Yayin da aka tambaye shi kan menene gaskiyar ganawar da aka ce ya yi da Tinubu a Faransa, Kwankwaso ya ce:

“Eh haka ne, amma ba zan yi dogon jawabi a yanzu ba sai zuwa ranar Alhamis, zamu fitar da cikakken bayani kan ganwar. Kuma mun fara ganawa kenan, ku bari mu gama zaku ji komai.”

Haka nan yayin da aka tambaye shi har tsawon kwana nawa zasu kwashe suka wannan tattaunawa, tsohon gwamnan ya jaddada cewa mutane su yi hakuri zuwa lokacin da zasu gama.

Wannan ganawa dai ta haddasa cece kuce da martani kala daban-daban a faɗin Najeriya, inda aka fara raɗe-raɗi da yuwuwar Kwankwaso ya koma APC.

Haka zalika wasu majiyoyi sun nuna cewa Bola Tinubu ya yi wa tsohon gwamnan tayin kujerar Minista a gwamnatinsa, wacce zata kama aiki ranar 29 ga watan Mayu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here