Irin Kasurgumar Sata da Rashin Gaskiya da Suka Dabaibaye Najeriya ya Girgiza Buhari – Fadar Shugaban Kasa

 

Irin satar da ake tafkawa a Gwamnatin Najeriya ta ba har Shugaba Muhammadu Buhari mamaki.

Malam Garba Shehu ya ce dokar kasa tayi wa Mai gidansa dabaibayi wajen yakar barayin kasar nan.

Mai magana da bakin shugaban kasar ya ce har yau babu wanda ya yi wa Buhari shaidar rashin gaskiya.

Abuja – Fadar shugaban kasa ta nuna Muhammadu Buhari ya girgiza da ya ga irin kasurgumar sata da rashin gaskiya da suka dabaibaye Najeriya.

Mai girma Muhammadu Buhari ya shaida haka ne ta bakin Mai magana da yawunsa, Garba Shehu a lokacin da aka yi hira da shi a tashar Channels.

Malam Garba Shehu ya nuna lamarin rashin gaskiya a kasar ya wuce yadda mutane su ke tunani.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin zai yaki barayin gwamnati, har yanzu da yake shirin barin ofis, ba a shawo kan matsalar ba.

Mai magana da yawun shugaban kasar ya ce har gobe mai gidansa mutumin gaskiya ne kuma bai da wani asusu da ya boye kudi a ko ina a kasar waje.

Abin da Garba Shehu ya fada

“Idan ka tambayi shugaban kasa (Muhammadu Buhari) wannan tambaya (meyasa har yanzu ake fama da rashin gaskiya a kasar nan) Shi ma zai ce ya na mamakin yadda wadanda ya kamata a ce su na gidan yari, su na tuka Rolls Toyce, su na yawo a cikin jiragen sama. – Garba Shehu

A dokar kasa, Garba Shehu ya ce babu abin da bangaren zartarwa zai iya illa ya yi bincike, sannan a gurfanar da duk wanda ake zargi da rashin gaskiya.

Hadimin shugaban kasar ya ce daga an kai magana zuwa kotu, su kuma sun gama na su kokarin.

An rahoto Mai magana da bakin shugaba mai barin-gadon ya na cewa kotu ce za ta iya yankewa mutum hukunci idan ya na da laifi ko kuwa akasin haka.

A gwamnatin Buhari ana binciken har manyan gwamnati, Shehu ya ce hakan ya nuna gwamnati mai-ci ta yi bakin kokarinta wajen yakar rashin gaskiya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here