Jirgin Ruwa ya Kife a Tekun Indiya ɗauke da Mutane 39

 

Rahotanni da ke fitowa daga ƙasar China na nuna cewa wani jirgin ruwa na kamun kifi mai ɗauke da mutum 39 ya kife a tekun Indiya.

Shugaba Xi Jinping ya bayar da umarnin yin dukkan mai yiwuwa domin tsamo mutanen.

Ana tsammanin akwai ƴan China 17 daga cikin mutanen 39 da ‘yan Indonesia 17 da kuma ‘yan Philiphines 5.

China da ta kasance ƙasar da ta fi ko wacce a duniya ruwa mai zurfi da ake kamun kifi cikinsa, ta tura manyan jiragen ruwa guda biyu domin gudanar da aikin ceto.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here