Hayakin Janareto ya yi Sanadin Mutuwar ɗalibai Biyu a Lokoja
Wasu daliban kwalejin fasaha ta Lokoja da ke jihar Kogi sun mutu sakamakon shakar hayakin janareto da suka kunna wanda ya cika dakinsu.
Read Also:
Kakakin ‘yansanda a jihar ta Kogi SP William Ovye Aya ya tabbatar wa gidan talabijin na Channels faruwar lamarin, inda ya ce salansar janaretan ya kasance yana fuskantar tagar ɗakin da suke kwana.
Sannan ya ce akwai daliba guda daya da ke kwance a dakin ita ma wadda ba ta rasa ranta ba, inda yanzu take kwance a asibiti.
SP William Ovye Aya, ya ce daliban da suka mutu sun hada da Bilikisu Tijjani Eleojo, mai shekaru 20, da Ibrahim Haliru mai shekaru 26, sai Mercy Ojochegbe wadda ke kwance a asibiti.