Matsin Rayuwa/Rashin Tsaro: An Gudanar da Zanga-Zanga a Jihar Osun

 

Mutane da dama sun fito kan tituna a garin Osogbo na jihar Osun domin gudanar da zanga-zanga kan matsin rayuwa da ƴan Najeriya ke fama shi.

Matasan da suka yi zanga-zangar sun buƙaci gwamnati ta magance halin ƙunci da al’ummar Najeriya suka faɗa ciki a baya-bayan nan.

Masu zanga-zangar sun fito ne ɗauke da katakai da kwalaye ƙunshe da saƙonni daban-daban.

Duk da cewa an jibge jami’an ƴansanda da dama kan titunan, hakan bai hana masu zanga-zangar ci gaba da tattakin nasu ba.

Lokacin da ya zanta da manema labaru, shugaban gamayyar ƙungiyoyin farar hula na jihar, Waheed Lawal ya nuna takaici kan yadda matsalar tsaro ke ƙara ƙamari a jihar da faɗin Najeriya.

Ya ce “wajibi ne gwamnati ta ɗauki matakan da suka dace, dole ne su nemo hanyar da al’umma za su riƙa rayuwa cikin kwanciyar hankali.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com