Shugaba Tinubu ya Sanya Hannu Kan Sabuwar Dokar Lantarki da aka yi wa Gyara

 

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanya hannu kan sabuwar dokar lantarki da aka yi wa gyaran fuska.

Dokar – wadda majalisun dokokin ƙasar biyu suka amince da ita a shekarar da ta gabata – na buƙatar magance matsalolin muhalli da yankunan da ake samar da lantarkin ke fuskanta.

Cikin wata sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasan, Ajuri Ngelale, ya fitar, ya ce sabuwar dokar ta yi tanadin cewar za a riƙa ware kashi biyar cikin 100 na abinda kamfanonin samar da lantarkin ke samu a shekara domin gina ababen more rayuwa a yankunan.

Haka kuma sabuwar dokar ta yi tanadin samar da wani asusu na musamman da al’ummar yankunan da haɗin gwiwar kamfanonin samar da lantarkin za su gudanar, don gina abubuwan maore rayuwa a yankunan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com