Jan Hankali ga `Yan Uwana `Yan Kwankwasiyya – Nazeer A Adam

Bari na fara da tariya;

A lokacin da Allah ya karbi rayuwar Kakan mu, ma’ana mahaifin jagora Engr. Rabiu Musa Kwankwaso, Mai girma Majidadin Kano Alh. Musa Saleh, a cikin wadanda mukayi mamakin halartarsu Miller road domin yiwa Jagora gaisuwa akwai Mai martaba Sarkin Kano Alh. Ado Bayero da sauran yan uwansa, duk da a al’ada ba mu saba ganin Sarkin kano yana zuwa ta’aziyya ba, wanda a lokacin dukkan mu da mukewa bin tsarin kwankwasiyya mun ji dadin wannan karamcin, kuma haka ya sanyayawa ran mu, da yawan mu munyi posting domin nuna jin dadin mu. WANNAN KARAMCI NE.

Ranar da Mai girma gwamna Alh. Abba Kabir Yusuf ya ziyarci fadar mai martaba sarkin kano a zagayen yakin neman zabe, kowa ya shaida irin Karamcin da Mai martaba Sarki ya nuna wa tawagar mu, wanda a wannan lokacin ma mun cika duniya muna fadin tarbar mutunci da mai martaba Sarki yai mana. ANAN MA AN MANA KARAMCI.

Me ya biyo baya ??

Ranar da aka yi bikin rantsuwar mai girma gwamna a filin kwallon kafa na kofar mata, Mai martaba Sarkin kano Alh. Aminu Ado Bayero da Dan uwansa Sarkin Bichi Alh. Nasir Ado Bayero sun halarci taron rantsuwa, wanda a nan filin taro aka samu wasu suna jifa da ihu da nuna rashin da’a a garesu, wanda duniya ta ga yadda Jagora ya nuna fushinsa a wajen, wadda har sai da ta kai ga Jagora ya rako Sarki zuwa mota domin nuna baya tare da wannan rashin albarkar da wasu suka aikata, Amma su waye suka aikata haka ?? Ku biyo ni a gaba.

Ranar da Mai girma gwamna zai sake bude asibitin Hasiya Bayero wanda aka kwato daga hannun wasu marasa kishi, anan ma mai martaba Sarkin kano Alh.Aminu Ado Bayero ya halarci bikin bude asibitin, amma anan ma aka sake samun wasu suka aikata rashin da’a ta hanyar yiwa Sarki Ihu da kunna wakokin da zasu bakantawa Sarki. Wanda anan kowa yaga yadda Mai girma gwamna Alh. Abba kabir Yusuf ya leko ta saman mota yana nuna fushinsa ga matasan da suka aikata wannan rashin da’ar. Wanda daga baya hukumar yan sanda ya gabatar da bincike akan wannan marasa tarbiyyar, inda aka a cikin wadanda aka kama, an wallafa vedionsu a shafin mai magana da yawun hukumar yan sanda reshen jihar kano, kuma anan duniya ta shaida cewa wasu yara ne, masoyan Mai girma tsohon Sarkin kano Muhammadu Sunusi ne suke shiga rigar mu ta kwankwasiyya domin aikatawa sarkin kano Aminu rashin da’a.

A abubuwan nan da na jero guda hudu, ta bayyana a fili cewa Da Jagora da Mai girma gwamna basa goyon bayan yadda ake shiga rigar mu ta kwankwasiyya domin cimma wata manufa.

Tunda anyi walkiya, mun ga kowa, To WALLAHIL AZEEM lokacin da wasu marasa mutunci zasu cigaba da shiga rigar mu ta kwankwasiyya su aikata rashin da’a ya wuce, Ba zamu zuba ido ba, Mun dai na bari

Na san da yawa zasuyi mamakin fitowar kalaman nan daga bakina ko ??

To bari na sake jaddada muku, NI DAN KWANKWASIYYA NE CIKAKKE.

Idan kuma akwai wanda zai min gorin bawa kwankwasiyya gudunmawa, to Bismillah.

Sai kun jini a Karo na biyu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com