Hukuncin da Kotu ta Yanke wa Mutumin da ya Cinnawa Mahaifiyarsa Wuta
Babbar jojin jihar Niger ya yake hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wani matashi da ya kashe mahaifiyarsa ta hanyar cinna mata wuta.
A watan Disamba 2021 ne matashin mai suna Stephen Jiya ya kashe mahaifiyarsa mai shekaru 61 bisa zarginta da silar bacewar matarsa a Suleja.
A ranar 23 ga watan Nuwamba, 2022 ne aka fara shari’ar Jiya bayan gurfanar da shi gaban mai shari’ar a ranar 14 ga watan Satumba, 2022.
Read Also:
Jihar Niger – Kotu ta yanke wa wani matashi dan shekaru 39, Stephen Jiya hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kama shi da laifin cinnawa mahaifiyarsa wuta har ta mutu a cikin watan Disamba 2021.
Jiya ya kashe mahaifiyarsa mai shekaru 61, Mrs Comfort Jiya, wata tsohuwar darakta a ma’aikatar ilimi ta jihar Niger kan zarginta da silar bacewar matarsa a Suleja.
Dokar da ta yanke hukuncin kisa kan Stephen Jiya
Premimun Times ta ruwaito babbar jojin jihar Niger, Mai Shari’a Halima Ibrahim Abdulmalik, wacce ta yanke hukunci kan Jiya, ta ce ta same shi da laifin kisan kai karkashin sashe na 221 da ke a kundin dokar final.
An gurfanar da Jiya gaban babban jojin a ranar 14 ga watan Satumba, 2022, yayin da aka fara sauraron shari’ar ta sa a ranar 23 ga watan Nuwamba, 2022, rahoton The Nation.