Rikicin Siyasa: Ƙarin Kwamishinonin Jihar Rivers Sun Ajiye Aiki

Wasu kwamishinonin Rivers shida sun sake ajiye aiki yayin da rikicin siyasa ke daɗa ƙamari a jihar.

Kwamishinan sufuri na jihar, Dr Jacobson B Nbina da kwamishinan ilimi, Farfesa Prince Chinedu da kwamishinar gidaje, Gift Worlu na daga cikin kwamishinonin da suka miƙa takardar ajiye aikinsu a baya-bayan nan.

Kwamishinan shari’a Prof Zacchaeus Adangor shi ne jami’i na farko da ya sanar da ajiye aikinsa.

Kwamishinan ayyuka a takardar ajiye aikin, ya ce ya ɗauki matakin ne bayan dogon nazarin da ya yi. Ya miƙa godiyarsa ga gwamnan tare da yi masa fatan alheri.

Sai dai kwamishinan kuɗi,Isaac Kamalu, a nasa ɓangaren bai faɗi dalilinsa na ajiye aiki ba.

A ɓangarenta, kwamishinar kula da walwalar al’umma ta yi wa gwamnatin ta Siminalayi Fubara fatan alheri inda ita ma ta ce ta ɗauki matakin ne bisa raɗin kanta da kuma wasu dalilai da suka buƙaci hakan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com