Wasannin 2024: FIFA ta Amince Rafari 30 ‘Yan Najeriya da su yi Alƙalanci

 

Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya, Fifa ta amince rafari 30 ƴan Najeriya su yi alƙalanci a wasanni daban daban na duniya a shekara mai kamawa.

Kakakin hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, Ademola Olajire ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa jiya Alhamis.

Ya cealƙalan wasan sun haɗa da Basheer Salisu da Ogabor Odey Joseph da Olufunmilayo Abigeal Alaba da Nuruddeen Abubakar da Abdulsalam Kasimu Abiola.

Jami’an ƙwallon ƙafar Najeriya ba sa samun shiga wasannin duniya har da gasar Afcon da za a yi a Ivory Coast.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com