Hukuncin da Kotu ta Yanke wa Matar da Take Satar Kananan Yara
Wata kotu a birnin Beira na kasar Mozambican ta yanke wa wata mata hukuncin daurin shekara 30 a gidan yari, da kuma biyan tarar dala 3,100, sakamakon samunta da laifin sace wasu kananan yara guda biyu domin neman kudin fansa.
Read Also:
A watan Oktoban bara ne matar mai shekara 37, ta sace wani yaro mai shekarar 14, inda ta nemi kudin fansa kusan dala 313.
Haka kuma ta kara sace wani yaron a watan Disamba, inda ta nemi kudin fansa dala 390.
Alkalin kotun ya ce ”Abu guda daya da za a yi domin kawar da aikata irin wannan laifi, shi ne zartar da hukuncin da doka ta tanada a kan duk wanda ya aikata makamancinsa”.