IATA ta Gargadi Najeriya Kan Rike Kudaden Jiragen Saman Kasashen Waje

 

Kungiyar da ke kula da zirga-zirgar jiragen sama ta duniya IATA, ta yi gargadin cewa gazawar Najeriya na biyan kamfanonin jiragen sama na kasashen waje dala miliyan 464, zai iya janyo wa tattalin arzikin kasar kara shiga mawuyacin hali.

A cikin wata sanarwa a shafinta na tiwita,kungiyar ta bayyana rike dala miliyan 464 na kamfanonin jiragen saman kasashen waje da Najeriya ta yi saboda karancin takardun kudi na na dala a matsayin abin takaici.

A don haka ne kungiyar ta ce matukar gwamnatin Najeriyar ta ki mayar wa kamfanonin jiragen saman kudadensu, to ko shakka ba bu abin zai janyo wa tattalin arzikin kasar babbar matsala.

A kalla dala miliyan 600 mallakin kamfanonin jiragen sama na kasashen waje 20 ne Najeriya ke rike da su tun daga farkon shekarar da muke ciki saboda ya kamata a bayar da su a dalar Amurka, a bar da ke karanci yanzu haka a kasar.

A cikin wadannan kudaden da Najeriyar ta rike, Emirates ya ce dala miliyan 85 na sa ne.

A ranar Litinin din data wuce, kamfanin jiragen saman na Emirates ya rage zirga-zirgarsa daga sau 11 zuwa 7 a cikin mako a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Legas.

Cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na kungiyar a Najeriyar ya fitar, ya ce kamfanin Emirates ya yi zargin cewa duk wani yunkuri da ya yi a kan fitar da kudinsa ya ci tura., hakan ne ya harzuka shi daukar matakin dakatar da zirga-zirga a Najeriya.

Kungiyar ta IATA, ta yi gargadin cewa rashin fitar da kudaden zai yi illa ga kamfanonin jiragen sama na kasashen wajen zai rage tafiye tafiyen jiragen saman kasashen waje a kasar.

Daga karshe kungiyar ta ce akwai bukatar gwamnatin Najeriya ta mai da hankali wajen biyan kudaden tun kafin lokaci ya kure mata.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here