Guguwa ta yi Sanadin Mutuwar Mutane 12 da Yara 3 a Turai

 

Wata guguwa mai karfin gaske da ta afka wasu yankunan Turai, ta yi sanadin mutuwar mutum 12 ciki har da yara uku.

Yawancin wadanda suka mutun sun fado ne daga bishiya a Italiya da Austria da kuma wasu a tsibirin Corsica na Faransa.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da iska sun kuma lalata tsibirin, yayin da ababan hawa kuma ke yawo kan ruwa.

Tsawar ta afku ne bayan shafe makonni ana tsananin zafi da fari a wasu sassa na Turai.

A tsibirin Corsica, iska mai karfin gaske da aka yi ta tunbuke bishiyoyi da dama da kuma lalata gidaje.

A wannan tsibiri ne mahukunta suka ce guguwar ta yi sanadin mutuwar wata yarinya ‘yar shekara 13 da bishiya ta fado mata.

Kazalika wani mutum dan shekara 46 ma ya mutu a irin wannan yanayin, yayin da wata mata mai shekara 70 kuma ta mutu bayan da motarta da daki wani waje.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here