ICC ta Fara Bincike Kan Zanga-zangar EndSARS

 

   Kotun hukunta masu manyan laifuka ta duniya wato ICC ta tabbatar wa BBC cewa ta fara gudanar da binciken farko dangane da rikicin EndSARS da ya faru a Najeriya.

Cikin wata sanarwa, ofishin mai shigar da kara na ICC ya ce ya samu bayanai kan laifukan da ake zargin an aikata yayin zanga-zangar da ta rikiɗe ta koma rikici.

Masu zanga-zangar sun shafe makonni masu yawa a titunan biranen ƙasar suna zanga-zangar adawa da cin zarafin da ake zargin jami’an ‘yan sanda na yi.

Kimanin fararen hula 51, da ‘yan sanda 11 da sojoji bakwai aka kashe, a cewar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

A nata ɓangaren kuma kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta ce jami’an tsaro sun buɗe wuta kan masu zanga-zangar, inda suka kashe tare da jikkata wasunsu da dama.

‘Yan sanda da sojoji duk sun yi watsi da zargin na Amnesty, sai dai ICC ta ce za ta bayyana sakamakon bincikenta na farko ga jama’a.

Yadda zanga-zangar ta koma rikici

Zanga-zangar ta EndSARS wadda aka fara a Legas da Abuja, ta kuma fantsama zuwa wasu jihohin kasar, kafin daga bisani ta rikiɗe ta koma rikici, abun da ya janyo asarar rayuka da dukiyoyin jama’a.

Wasu ɓata gari da ake zargin sun fake da zanga-zangar sun rika rusa gine-ginen gwamnati da na wasu ‘yan siyasa musamman a jihar Legas, da ke kudu maso yammacin kasar.

Hukumomi sun baza jami’an ƴan sandan kwantar da tarzoma domin shawo kan lamarin, sai dai tashin hankali ya ci gaba da ƙaruwa sakamakon kisan masu zanga-zanga a Lekki.

Masu zanga-zangar sun zargi jami’an tsaro da buɗe masu wuta a Lekki da ke jihar Legas, wato cibiyar inda ake gudanar da zanga-zanar, abin da ya janyo jikkatar mutane da dama.

Wasu dai na ganin buɗewa masu zanga-zangar wuta ya taimaka wajen kazantuwar lamarin musamman a jihar ta Legas.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here