Ƙabilar Igbo ta Nesanta Kanta Daga Ikirarin IPOB kan zanga-zangar ENDSARS

Ƙungiyar ƙabilar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo, ta nesanta al’ummarta daga wasu maganganun da shugaban ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu ya yi wanda ke goyon bayan lalata kadarorin Yarabawa a Legas.

Cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar Cif Nnia Nwodo ya fitar, ya ce Ohanaeze ta fusata da yadda kalaman shugaban na IPOB din yake ƙoƙarin tunzura jama’a kan zanga-zanga EndSARS a Legas.

Shugaban ƙungiyar ta IPOB wadda gwamnatin Najeriya ta haramta, Nnamdi Kanu ya fito a kafafen sada zumunta yana bayanin da mutane da dama za su iya fassara shi a matsayin wanda zai iya tunzura jama’a su dauki doka a hannunsu.

“Su na tunanin za su iya yi mana barazana kamar yadda suka saba yi a baya. Yanzu muna shekara ta 2020 ne, matasa baza su lamunci duk wani shashanci ba. Don haka ya isa haka, babu gudu ba ja da baya.” Inji shi.

Wannan dai kadan kenan daga cikin irin maganganun da Nnamdi Kanu ya yi wanda yasa ƙungiyar ta Ohanaeze nesanta kanta da kalaman.

Cif Nnia Nwodo, ya ce wannan sanarwar da ya fitar tana da ban takaici saboda abin da ta kunsa ba kawai ƙarairayi ba ne, an kitsa ta ne domin a kawo cikas daga dadaddiyar alakar da ke tsakanin kabilar Igbo da kuma Yarabawa.

Haka kuma a cewar Ohanaeze tana jin babban makasudun wannan maganganun na Nnamdi mai tayar da hankali ya yi shi ne don ya haifar da rarrabuwa kai da tarzoma, lamarin da Ndigbo ta ce baza su lamunta ba.

Ƙungiyar al’ummar Igbo cikin kakkausar murya ta musanta zargin cewa akwai hannun matasan Igbo da ke Lagos a zanga-zangar #Endsars kuma wai sun yi hakan ne da wata babbar manufa ta lalata tattalin arziƙin ƙasar Yarabawa.

Ta ce ai a bayyane take ƙarara cewa hankali ba zai ɗauki irin wannan tunani na cewa Igbo sun shirya wargaza tattalin arziƙin wata al’umma ba, bisa la’akari da ganin yadda suke da harkokin kasuwancinsu warwatse a kowanne sashe na Nijeriya.

A cewar Ohanaeze marar tunanin ne kaɗai zai yi kashi a inuwar da yake cikinta don rama wani abu da aka yi masa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here