Hukumar INEC ta ɗage Zaɓen Gwamna a Wasu Mazaɓun Jihar Legas

 

Hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC ta ɗage zaɓen gwamna da na ƴan majalisar jiha a mazaɓu 10 da ke jihar Legas.

Wuraren da wannan ɗage war ta shafa sun haɗa da rukunin gidaje na Victoria Garden City (VGC) da ke ƙaramar hukumar Eti-Osa.

Yayin da yake magana da manema labarai, kwamishinan hukumar zaɓe a jihar ta Legas, Mista Olusegun Agbaje ya ce ma’aikatan wucen gadin da ke aiki a yankin sun ƙi gudanar da aikinsu saboda ƙalubalen da suka fuskanta a zaɓen shugaban ƙasa.

“Muna da mazaɓu takwas a nan da masu zaɓe 6,024 da aka yi wa rajista kuma daga cikinsu 5,624 sun karɓi katin zaɓensu,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa lamarin ya shafi wasu mazaɓu biyu a rukunin gidajen.

“Bayan tuntuɓa, mun sami umarni daga hukumar zaɓe ta ƙasar cewa mu ɗage zaɓen zuwa gobe Lahadi da ƙarfe 8:30.” kamar yadda kwamishinan hukumar zaɓn ya shaida.

bbnaija news

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com