NLC za ta Rufe Dukkanin Ofisoshin Babban Bankin Najeriya Kan ƙarancin Takardun Naira

 

Ƙungiyar ƙwadago ta NLC a Najeriya ta umarci ma’aikata su fara zanga-zanga a dukkanin ofisoshin babban bankin ƙasar tun daga mako mai zuwa saboda ƙarancin takardun naira da ake fama da shi.

Shugaban ƙungiyar Joe Ajaero, wanda ya yi wa manema labarai a Abuja bayani game da shirin, ya ce daga jibi Juma’a ne za su fara haɗuwa sannan kuma su fara rufe dukkanin harkokin kasuwanci daga ranar Laraba mai zuwa a faɗin ƙasar.

A ranar 13 ga watan nan na Maris ne ƙungiyar ta NLC ta bai wa gwamanatin tarayyar Najeriya wa’adin kwana bakwai na ta ɗauki matakan sassauta matsalar da ake fama da ita ta ƙarancin takardun kuɗin ƙasar na naira da kuma ƙarancin mai, ko kuma ta kira yajin aiki na ma’aikata.

Shugaban ya ce, matakin zanga-zangar shi ne abu na ƙarshe da ƙungiyar za ta ɗauka kasancewar ta bi dukkanin matakan da ya kamata ta bi na ganin an samu sassauci kan tsananin wahalar da ma’aikata da sauran ƴan Najeriya ke sha saboda ƙarancin takardun kuɗin amma abin ya gagara.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here