ISWAP: ‘Yan Ta’addan Sun Kashe Wasu Sojoji

 

Akalla Sojojin Najeriya 10 sun rasa rayukansu a harin da yan ta’addan ISWAP suka kai musu yankin Alagarno-Timbuktu dake jihar Borno, Arewa maso gabashin Najeriya.

A cewar AFP, bisa rahoton da ta samu, an kashe Sojojin 10 ne bayan harin kwanton baunan da aka kaiwa Sojojin ranan Litinin a Alagarno.

“Mun yi rashin Sojoji 10 a fada kuma yan ta’addan sun dauke daya,” majiyar ta bayyana.

A cewar wata majiyar kuwa, “An yi mumunan artabu kuma an kashe yan bindigan, amma sun galabe Sojojin.”

HumAngle ta ruwaito cewa Sojojin sun tafi sintiri ne yayinda suka yi arangama da yan ta’addan ISWAP a hanya.

An kwace manyan motocin yakin Sojojin Najeriya. Yan ta’addan sun kwace mota kirar Toyota Buffalo da sabuwar motar yaki KIA KLTV-181 da kamfanin Kia Motors ta kera.

An tattaro cewa yan watanni da suka gabata aka kaddamar da motar yakin kuma an ruwaito cewa tana da matsaloli musamman wajen amfani da ita a filin daga.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here