Na yi Iya Koƙarina ga ‘Yan Najeriya – Shugaba Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya mulki Najeriya da iyaƙar ƙokarinsa, inda ya ce bai ba wa ‘yan ƙasar kunya ba.
Shugaban wanda yaje jihar Bauchi a cigaba da ƴaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC na shugaban ƙasa da kuma na gwamna, ya bayyana hakane lokacin da ya kai ziyara gidan Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Suleiman Adamu.
Buhari ya ce dubban mutane da suke fitowa su tarbe shi a duk inda yaje na nuna ƙarara irin soyayyar da ake masa.
Read Also:
“Ina so na faɗa cewa tsakanin 2003 zuwa 2011, na kai ziyara dukkanin ƙananan hukumomin Najeriya, sannan a 2019, lokacin da nake neman sake komawa kan mulki ƙaro na biyu, na ziyarci dukkanin jihohi a faɗin ƙasar, mutanen da naga sun fito sun tarbe ni, abu ne da ba zan iya misaltawa ba saboda dandazonsu, a lokacin na yi alkawarin mulkar Najeriya da ‘yan Najeriya da iyaƙar ƙokarina kuma zuwa yanzu na san na yi ƙokari,” in ji shugaban.
Tun da farko a jawabinsa, Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Suleiman, ya ce abu mai kyau ne idan shugabannin siyasa suka nuna girmamawa ga Sarakuna da kuma masarautu ta hanyar kai musu ziyara.
Ya godewa shugaba Buhari kan irin ci gaban da gwamnatinsa ta kawo a Bauchi, inda ya ce aikin haƙo man fetur na Kolmani, wani bu ne da ‘yan jihar da ma arewa maso gabas ba za su manta ba.