Hukuncin da Kotun Rwanda ta Yanke wa Tsohon Ministan Matasa da Al’Adu na Kasar

 

 

Wata babbar kotu a kasar Rwanda ta yanke wa wani tsohon ministan matasa da al’adu ɗaurin shekaru biyar a gidan yari bisa samunsa da laifin cin hanci da rashawa, inda ta tsawaita hukuncin da aka yanke masa a baya da shekara guda.

Hukuncin asali, wanda ya zo a bara, a kan Edouard Bamporiki, wani lamari ne da ba kasafai ake samunsa ba na wani babban jami’in da aka samu da laifin cin hanci da rashawa a kasar.

A watan Mayun da ya gabata ne aka dakatar da shi daga mukaminsa, inda aka masa ɗaurin talala yayin da ake bincikensa da laifin almundahana. Ya kasance cikin ɗaurin talalal har zuwa lokacin da aka yanke hukuncin.

Bamporiki ya amsa laifin da ake zarginsa da shi a shafinsa na Twitter, sannan ya roki shugaba Paul Kagame da ya gafarta masa, amma a watan Satumba wata kotu ta yanke masa hukuncin shekaru hudu – wanda ya daukaka kara.

A ranar Litinin, alkalin wata babbar kotu a Kigali babban birnin kasar, ya ce dokar ta yi aikinta saboda hakan ya zama izina ga wasu.

Mai wakokin baƙan mai shekara 39 da haihuwa wadda kuma mai shirya fina-finai a baya, ya kasance babban mai goyon bayan shugaba Kagame da jam’iyya mai mulki kuma ya yi fice cikin lokaci kankani.

Lauyan sa, Evode Kayitana, ya shaida wa BBC cewa ba su yanke shawara kan ko za su daukaka kara ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here