Babban Sifeton ‘Yan Sandan Najeriya ya Bayar da N2bn ga Iyalan ‘Yan Sandan da Suka Mutu
Babban sifeton ‘yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya bayar da chek din naira biliyan 2.08 ga iyalan ‘yan sandan da suka mutu a bakin aiki cikin shekara biyar da suka gabata.
Cikin wata sanarwa da mai magana yawun rundunar ‘yan sandan ƙasar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ya ce an bayar da chekin kuɗin ga mutum 785 da za su amfana da kuɗaɗen.
Read Also:
“Rundunar ‘yan sandan Najeriya, ta hanyar ofishin kula da inshora, ya samu damar warware haƙƙoƙin mamata kusan 2,533 wanda ya kama kusan naira biliyan 6.01 tsakanin watan Yunin 2023 zuwa yau”, in ji sanarwar.
Babban sifeton ‘yan sandan ya kuma yaba wa shugaban ƙasar Bola Tinubu, saboda sanya walwalar ‘yan sanda cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba.
A Najeriya dai iyalan jami’an tsaro kan shiga tasku bayan mutuwar iyayensu ko mazajensu waɗanda suka sadaukar da rayukansu wajen bauta wa ƙasar.