Gwamnatin Kano za ta ga Abin da ya fi Dacewa Tsakanin Gyara ko Rusa Masarautu – Kwankwaso
Rabiu Musa Kwankwaso ya yi hira da manema labarai daga isowansa garin Kano a tsakiyar makon nan.
Babban ‘dan siyasar ya tofa albarkacin bakinsa a game da masarautun da gwamnatin APC ta kirkiro.
Kwankwaso yana ganin nan gaba dole gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta zauna a game da wannan batu.
Kano – Rabiu Musa Kwankwaso ya yi doguwar hira da manema labarai a ranar Alhamis, 18 ga watan Junairu 2023 a Kano.
Tashar rediyon Nasara FM tana cikin wadanda suka dauko hirar kai-tsaye da aka yi da jagora kuma ‘dan takaran na NNPP a 2023.
A tattaunawar da aka yi da shi, Rabiu Musa Kwankwaso ya tabo batun masarautun da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta kafa.
Kwankwaso, Abba da masarautun Kano Tsohon gwamnan ya bayyana cewa ba a taba yin zama da shi domin tattauna makomar masarautun ba, amma ya ce ya san za ayi.
Rabiu Kwankwaso ya nuna gwamnatin Abba Kabir Yusuf da NNPP za ta dauki matakin da ya dace a game da sababbin masarautun.
Read Also:
Kwankwaso ya ce tarko aka shirya da masarautu
Legit Hausa ta bibiyi hirar da aka yi da magudun darikar ta Kwankwasiyya, mun ji yana zargin gwamnatin da ta wuce da mugun nufi.
Duk da haka, Sanata Kwankwaso ya ce wani lokacin a kan iya kawo mugun tsari amma ya amfanar ko kuwa a ci karo da akasin haka.
‘Dan takaran shugaban kasar na zaben 2023 yake cewa tarko aka shirya wajen kirkiro sarakuna a Rano, Bichi, Gaya da kuma Karaye.
Kano: Muhammadu Sanusi II zai dawo?
Kwankwaso ya shaidawa ‘yan jarida cewa gwamnatin jihar Kano za ta ga abin da ya fi dacewa tsakanin gyara ko kuwa rusa masarautun.
Ana ta rade-radin gwamnatin NNPP mai-ci za ta maido Muhammadu Sanusi II. Tsohon sanatan na tsakiyar Kano bai bayyana matakin da za a dauka ba, amma ya nuna za ayi abin da zai fi zama alheri ga al’umma.
Abin da Rabiu Kwankwaso ya fada
“Amma na san dole za a zo ayi magana, a ga menene ya kamata a yi, ta ina za a bullo.
“Ya za ayi? Haka za a bari? Gyara za ayi? Rusau za ayi? Za a zo a duba. Abin da ya kamata ayi, shi za ayi.”
– Rabiu Musa Kwankwaso