Jami’ar Abuja za ta Hada Kai da NDLEA Don Fara Gwajin Kwayoyi Kafin Bai wa Dalibi Gurbin Karatu

 

Jami’ar birnin Tarayya za ta fara gwajin kwayoyi kafin bai wa ko wane dalibi gurbin karatu a nan gaba.

Shugaban Jami’ar, Farfesa Abdul-Rasheed Na’ Allah shi ya bayyana haka inda ya ce za su hada kai da Hukumar NDLEA.

Hukumar Kula da Jami’o’i a Najeriya (NUC) ta amince da karin tsangayoyi 26 ga Jami’ar ta Abuja.

FCT, Abuja – Shugaban Jami’ar Abuja, Farfesa Abdul-Rasheed Na’ Allah ya ce duk dalibin da ke neman gurbin karatu sai an yi ma sa gwajin kwayoyi.

Farfesa Na’ Allah ya ce Jami’ar na bukatar sanin halin dalibai game da kwayoyi don taimaka musu watsar da ita.

Wace doka aka saka a Jami’ar Abuja kafin samun gurbin karatu? Farfesan ya bayyana haka ne yayin shirye-shiryen bikin yaye dalibai karo na 27 a ranar Laraba 4 ga watan Oktoba, Daily Trust ta tattaro.

Ya ce za su hada kai da Hukumar NDLEA don taimakawa dalibai da ke ta’ammali da kwayoyi barinta don kada su addabi jama’a bayan kammala karatu.

Ya ce yayin bikin, Jami’ar za ta yaye dalibai masu digirin digirgir guda 100 sai kuma masu digiri na biyu mutum fiye da 700.

Dalibai nawa za a yaye a Jami’ar Abuja?

Ya kara da cewa akwai kuma dalibai fiye da dubu bakwai da za a yaye su a ranar Asabar yayin bikin da su ka kammala digiri dinsu a Jami’ar.

Na’ Allah ya ce a yanzu sun inganta Jami’ar ta dawo ta duniya inda su ke da tsangayun yarukan duniya kamar Faransanci da Japananci da kuma yaren Portugal.

Ya ce Jami’ar ta mai da koyan daya daga cikin yarukan wajibi ga ko wane dalibi kafin kammala digiri, cewar TheCable.

Hukumar Kula da Jami’o’in Najeriya (NUC) ta amince da karin tsangayoyi 26 ga Jami’ar don inganta ilimi.

Dole dalibi ya mallaki kamfani kafin kammala digiri, Farfesa Na’Allah

A wani labarin, shugaban Jami’ar Abuja, Farfesa Abdul-Rasheed Na’Allah ya ce dole dalibi ya mallaki kamfani kafin kammala karatu a Jami’ar.

Farfesan ya ce wannan doka ta zama dole don inganta rayuwar matasa bayan kammala karatu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com